Labarin Wani Attajiri Hashimu
idan kazo neman bashi awajansa baze ta6a baka a idon mutaneba seya ke6e dakai gefe sana ya baka.
idan kazo maidowa ka bashi acikin mutane to daga ranar ko iyayanku daya daya dashi baze kara baka bashiba, kuma idan ya baka rance to daga rannan ya mance dakai sede inka maido dan kanka.
kasan al'adar bahaushe da anga mutun ya samu wadata za'a fara zundensa, shima haka takasance dashi wasu sukace dodon kudi garai wasu sukace aljanar kudi garai amma abin ko damunsa bayayi.
Yana daga cikin al'adarsa shine idan ya aminta dakai seya aurama daya daga cikin ya'yansa kyauta ya baka gona babba kyauta, sannan ya warema shanu masu yawa karinka kiwo idan uku suka haihu kana da biyu yanada daya.
yanada da wata yarsa kyakykyawa wanda yafiso acikin dukkan y'a'yansa me suna (SANTALA) itama ya aurar da ita kamar yadda yake a a'ladarsa, amma ita shanun daya bata ita da mijinta sun linka wadanda ya saba bayarwa ga yayansa domin seda ya bata ninki uku kan yadda yakeba yayansa idan ya aurar dasu.
dan adam butulu katsam rana daya aka nemeta itada mijnta da tarin shanun aka rasa, da aka gayama se yace sun yiwa kansu, akwana atashi hausawa na cewa KOMIN NISAN DARE LALLE GARI ZE WAYE seda akayi shekaru (18) kwatsam sega yar nan tasa tadawo, TIRKASHI! babban abin mamaki shine batare da mijintaba sannan ba shanuba komi tare daita daga ita se yayanta biyu yunwa duk ta cinyesu ................
zan cigab kaidai rinka shiga site dinnan akai akai anyishine domin ku
nagode kuma kayi share dan allah
No comments