Madigo da illolinsa-
Abubuwa Goma Dake Jawo Mata Suke Fadawa Dabi'ar Madigo
Yana da Kyau masu karatu suma fahimci shi Madigo din nan yaya ma ake yinsa domin wajen hana jawo shi.
Duk wani nauyin da maza kanbi domin gamsar da mace su ne hanyoyin da 'yan madigo suke bi domin gamsar da junansu. Kama daga shafe shafen jikunan junansu, sumbata, sakace juna, lasar al'aurar juna, goge da kuma amfani da azakarin roba domin biyawa juna bukata..
Wadannan sune aiyuka na aikace a zahiri da mata 'yan Madigo suke bi. Ga kuma wasu daga cikin hanyoyin dake musu hakan:

1: Al'adun Makaratu: Kamar yadda nayi bayani a baya, al'adar nan na mummy da Darling daya samu zama a makarantu kwana harma da makarantun jeka ki dawo na mata tabbas ya baiwa damar 'ya'ya mata shiga harkar madigo sosai. Inda za a ga yadda manyansu a aji suke jawo kananan na kasa dasu da sunan daughter tace daga nan kuma sannun a hankali a soma cusa mata ra'ayi har sai an soma aikata madigo da Ita kamin itama ta zama siniya bayan tasan harkar ta jawo na kasa da Ita.
Kashi 80 na 'yan matan da suka shiga harkar madigo ta irin wannan al'adar makaratun ne suka tsinci Kansu a cikin. Duk wacce tayi makarantar kwanan ko da kuma Allah Ya kareta bata taba yi ba to tabbas tasan anayi ko ma tana gani anayi a gabanta.

2:Tashen Balaga: A wannan lokacin ne iyaye ya kamata su sanyawa 'ya'yansu idanu sosai. Domin a wannan lokacin ne ko 'ya'ya maza suke iya tsintar kansu a zina ko luwadi. Domin a wannan yananyin mace mai tashen balaga bazata yi wahalar yaudaruwa ba ga abunda yafi samuwa na biyan bukatar mafi kusa da Ita. Idan maza ne sukafi saukin ta samo ta kuma soma jima'i da jin dadinsa shi kenan ta zama mazinaciya, idan da kuma madigo ta soma jin dadi to Ita da maza a wannan lokacin sai anyi dagaske. A irin wannan yanayin mata 'yan madigo suke yaudarar yara mata su jefasu cikin al'amarin cikin sauki da sauri kuma a arha ba sai sunyi hidimar kashe kudi ba ganin Ita mai tashen balaga babu abunda ya dameta illa kawai ta samu biyan bukata tayi gama. Don haka dole ne iyaye su kula sosai da irin wadanda 'ya'yansu suke mu'amala dasu a lokacin da suka kai shekarunsu na tashen balaga.
3: Cudanya: Yi mu'amala da 'yan madigo yana jawo hankalin yara mata suma su fada yi. Dole ne ki kauracewa mata masu wannan dabi'ar saboda yawan mu'amala ko cudanya dasu a kwana a tashi suna iya jefaki.
4: Gudun Samu Ciki Ko Cuta. Mata da dama an yaudaresu ne da shiga harkar madigo da nuna musu cewa bazasu yi ciki ba ga kuma samun biyan bukata haka zalika babu ruwansu da daukar wata cuta da ake samunsu daga saduwar mace da miji. Wannan hudubar yayi matukar tasirin ga 'ya'ya mata kanana da suke da sha'awar jima'i kuma suna gudun shigan ciki ko kamuwa da wata cuta.
5: Kadaita: Ba kamar maza ba, anfi samun kwanciyar hankali da aka ga 'ya'ya mata sun kule kawunansu a daki suna hira, babu wanda yake da yake daukar yin haka wani matsala ne ba kamar maza ba, muddin aka ga maza sun cika kebe kawunansu a kulle nan take zargi yake shiga. Haka kuma ba a daukarsa komai domin an ga mata biyu sun shiga wanka tare. Mata idan suka kadaita su ba wani abu bane su fitowa juna tsiraicinsu. Mata suna iya fitowa wanka tare kuma su shawa juna manshafawa a jiki duk wadannan kaidaitan da mata suke yi kuma an saba ganin a matsayin normal, hanyoyi ne masu saukin jefa mata madigo.
Mata sunfi maza sanin mace mai Kyau, mace tafi namiji saukin kamuwa da sha'awa idan taga jikin 'yar uwarta macen da take so ko da kuwa bata madigo haka suke. Shi yasa idan mace taga 'yar uwarta macen data kwanta mata a rai sai ta tabbatar da cewa ta fada mata tana sonta da kawa ko kuma ta ce mata kin mini kyau idan kuma 'yar madigo ce kai tsaye zata ce mata tana sonta.
Don haka dole ne a kiyaye a kuma sanya idanuwa a lokacin da mata zalla suka kadaice da junansu, a kuma hanasu duk wani abu da zai sa suna kallon tsiraicinsu.

6: Yawan sha'awa: Akwai mata da dama da suke da halittar yawan sha'awa. Sha'awanta yafi karfi Ita kanta. Irin wadannan matan ana samunsu a harkar madigo. Domin su muddin sha'awarsu ta mosta abunda ya soma samuwa dashi suke amfani, idan namiji ya samu tofa shine zai kwantar mata, haka kuwa a wannan yananyin nata idan macece mafi saukin samu da Ita za ayi harkar.
Irin wadannan matan suna nan kuma duk yadda sukayi kokarin dainawa yana musu wahala muddin ba sun auri mazan da suke iya gamsar dasu bane.
Irin wadannan matan suna nan kuma duk yadda sukayi kokarin dainawa yana musu wahala muddin ba sun auri mazan da suke iya gamsar dasu bane.
7: Kwadayin abun duniya: Kashi 60 cikin 100 a yanzu mata da suke shiga harkar madigo kwadayi ne da son abun duniya. Ganin yadda manyan mata masu wannan harkar suke musu hidima, yasa suka kasa dainawa domin son abun duniya. Wasu ma sam ba dadin harkar suke yi ba, amma da yake masu yi dasu suna basu kudi yasa bazasu iya dainawa ba kuma bazasu jawo wasu su shiga ba.
8: Rashin Samun Gamsuwa a wajen mazajensu: Duk macen data saba da Madigo kamin tayi aure yanada matukar wahala namiji ya gamsar da Ita muddin ba shi namijin yasan abunda ya aro bane daman can.
Madigo yana baiwa mata masu yinsa damar samun gamsuwa babu wani tantama anan. Domin suna samun lokacin mai tsawo ana musu wasa, haka kuma duk wasu lunguna na jikinta ana tabamatasu, muddin mace tayi aure ta kasa samun wannan to tabbas idan daman 'yar madigo ce zata ci gaba, idan kuwa batayi to ko dai idan ta samu dama ta soma, ko ta rika wasa da kanta daga inda mijinta ya kasa ko kuma ta samu wani bayan mijin nata yana biya mata bukata.
Ga irin mazan nan masu mari ka tashi, a cikin mintuna uku ko biyar sunyi zuwan kai, to da akwai hadarin matansu suna iya fadawa a dayan ukun da na ambata a baya.

9: Yawan Kallon bidio na karatun litattafai batsa: Babu shakka ci gaban zamanin yanzu ya taimaka wajen habaka wannan dabi'ar, domin wasu a bayama suna dai ji ana cewa madigo ne basu ma san yadda ake yinsa ba, yanzu sai gashi a hannunta, idan yau ta kalla gobe ta kalla jibi tana iya cewa bari ta gwada da wacce tasan tana yi ko tayi dana kusa da Ita. Don haka ci gaba na zamani ya kawo mana kalle-kalle da karance-karance da suka taimaka wajen yada harkar madigo.
10: Sakacin Magabata: Du kanmu iyaye dole mu dauki al'hakin yada wannan al'amarin ganin yadda wasu iyayen basu damu da kula da tarbiyan yaransu mata ba, basusan abokan huldarsu ba, babu ruwansu da wacce makaranta zasu sakasu bare suyi bibiyansu. Basu damu da inda yaransu suke shiga su fito ba. Babu ruwansu da wanda zasu aura yaransu barai su samu tabbacin irin tsaro da tarbiyan da zai daura daga inda su suka tsaya.
Zancen cusawa yaranmu tsoron Allah tun suna kanana yayi rauni wanda kuma shi ne babban hanyar da zai fitar damu cikin wannan bala'i da ya dosomu. 'Ya madigo sun daina kunya ko tsron kowa fitowa suke karara suce sune duk kuwa da doka ta dauri da ake dashi a wannan kasar, duk da kirayekiraye da malumma suke yi na aji tsoron Allah.
Wadannan da wasu da dama sune wasu hanyoyin da nake ganin suke jefa mata shiga madigo.
Allah Ya shiryar damu da zuri'armu baki daya ameen.

No comments