Header Ads

HUKUNCIN WANDA YAYI ZINA DA WACCE ZAI AURA!

Aslmu Alkm Wrhmtullh fatar katashi lfy Allah yasa haka ameen ya ibadah ya hakuri alagafatar malam daga Birnin kebbi nake, inada tmby Allah yabaka damar sanar dani ameen.


Tambaya ta itace inada yarinyar da zan aura amma kuma mun aikata abinda baidace ba sbd mun kusanci juna da ita kuma gashi bayan sallah zamuyi aure.


Malam minene hukunci aurenmu kuma muna bukatar mu gyara kada muyishi cikin fushin Allah wsslm malam Allah yakara sani ameen.

AMSA
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Babban abu na farko shine kuji tsoron Allah kuyi tuba ta gaskiya zuwa ga Ubangijinku. Domin hakika kun aikata babban kuskure kun aikata laifin da shine na biyu ko na uku acikin manyan kaba'irori a addinin Musulunci.


Bayan haka kuma wajibi ne gareta tayi istibra'i. Wato jini uku kafin auren da zakuyi, kamar yadda hukuncin yake a Mazhabin Malaman Madeenah.
Kuci gaba da neman gafarar Allah domin hakika Allah mai gafara ne kuma mai karbar tuban bayinsa ne.


Idan kuma ta riga ta samu ciki (juna biyu) ta dalilin zinar da kukayi, to bai halatta adaura muku aure ahaka ba. Kuma bai halatta a zubar dashi ba. Sai dai a jira bayan ta haihu adaura muku auren.


WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU

ZAKU IYA TURO DA TDMBAYOYINKU TA HANYAR TEXT (07064213990) KO EMAIL (zaurenfiqhu@gmail.com).

No comments

Powered by Blogger.