Masu yin WhatsApp za su fara biyan haraji a Uganda
Majalisar dokokin kasar Uganda ta amince da wata sabuwar doka wadda za ta fara cajan 'yan kasar da ke amfani da shafin sada zumunta na WhatsApp harajin shlillings 200 (kimanin naira 20) a kullum.
Har ila yau za su fara biyan harajin cinikayyan da suka yi ta wayar salula, wato kashi 1 cikin 100 na kudin da aka yi kowace cinikayya ta waya.
Dokar za ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Yulin bana.
Sai dai wadansu 'yan majalisa uku sun nuna adawarsu ga sabuwar dokar, inda suka bayyana sabuwar dokar da "karabar haraji kashi-kashi," kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito.
Yan majalisa Robert Kyaggulanyi da Joshua Anywarach da kuma Silas Aogon sun ce karin haraji zai zama wani take 'yancin masu amfani da WhatsApp saboda ana cajansu haraji kan katin wayar da suke saya.
Dan majalisar Arewacin Kasanda, Patrick Nsamba na jam'iyyar adawa, ya ce:
"Abu ne mai sauki dan majalisa ya ce harajin kaso 1 cikin 100 kudi ne kadan, amma ga mutanen da suke samun kasa da dala a rana, kudi harajin kudi ne mai yawa."
A galibin kasashen duniya ba a biyan haraji kafin amfani da kafar sada zumunta ta WhatsApp.
No comments