Header Ads

Me ya sa matasa ke kauracewa Facebook a Amurka?



Matasa a Amurka na kauracewa Facebook suna komawa wasu kafofin sada zumunta irinsu YouTube da Instagram da Snapchat, a cewar wani bincike.
Kashi 51 cikin 100 na matasa ne suke amfani da shafin Facebook.
Wannan ya nuna yawan matasan da ke amfani da Facebook ya ragu da kashi 20 cikin 100 tun daga shekarar 2015, kamar yadda wata cibiyar bincike ta Pew Research ta yi bincike a kan yadda matasa suke amfani da shafukan sada zumunta.
Akasarin matasa masu shekaru 13 zuwa 17 sun mallaki ko kuma suna da damar amfani da wayoyin komai da ruwanka masu intanet.
YouTube ya sha gaban Facebook wanda a baya ya fi samun karbuwa tsakanin matasa, inda kashi 85 cikin 100 na matasan suka fi so su rika amfani da shafin YouTube.
Instagram shi ne na biyu inda kashi 72 na matasa ke amfani da shafin, yayin da Snapchat ya kasance na uku inda kashi 69 na matasa suke amfani da shafin.
Sai dai babu sauyi a yawan matasan da ke amfani da shafin Twitter inda kawo yanzu kashi 32 ne suke amfani da shi.
Kashi 14 ne kuma ke amfani da shafin Tumblr idan aka kwatanta da sakamakon da aka gano a shekarar 2015.


Sai dai duk da cewa Facebook ya rasa matsayinsa tsakanin matasa ga kamfanin Google da ya mallaki YouTube, amma shi ne ya mallaki shafin Instagram da ke samun karbuwa.
Binciken da cibiyar Pew ta yi a kan matasa 750 a cikin wata guda a farkon shekarar da muke ciki, ya gano cewa karuwar da aka samu a yawan matasan da suka mallaki wayoyin tafi da gidanka ya taka muhimiyyar rawa a sauyin da aka samu.
A yanzu kashi 95 cikin 100 na matasa a Amurka sun mallaki wayoyin kansu idan aka kwatanta da kashi 73 a cikin shekaru uku da suka gabata, abin da ke nuna cewa an samu karuwa da maki 22.
Binciken ya kuma gano cewa yayin da akasarin matasa ke amfani da kafar sada zumunta iri daya da sauran takwarorinsu, amma matasa da iyayensu ma su karamin karfi ne, sun fi amfani da Facebok fiye da matasan da iyayensu masu hannu da shuni ne.
Sai dai binciken ya kasa bayyana irin tasirin da kafofin sada zumunta suke yi a rayuwar matasa.
Kusan kashi daya bisa uku na matasan sun bayyana cewa shafukan sada zumunta na tasiri a rayuwarsu yayin da kashi daya bisa hudu suka babu wani tasiri da suke yi.
Sai dai kashi 45 cikin 100 sun ce tasirinsu na da kyau kuma ba shi da kyau.


No comments

Powered by Blogger.