Header Ads

TAMBAYA AKAN NISABIN ZAKKAH :



Aslm alaikum Malam da fatar ka wuni cikin qoshin lpy bugu da qari ina miqa dubun gaisuwa mai tarin yawa da irin nasihohin da kake yimuna a kowane lokaci Allah ya saka maka da gidan Aljannah firdausee ya qara hazaka da nisan kwana .
Malam idan mutum yana kasuwanci shin sai kudin sa sun kai kamar dubu dari nawa zai fara fitar da zakka.?
Daga Usman Muhammad.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ita zakkar kudi bata wajabta akan mutum har sai ya mallaki kudin da yawansa yakai nisabi, kuma kudin yakai cikakkiyar shekara guda ahannunsa.
Nisabin zakkar abana (1439 bayan hijira) yakai kimanin Naira 1,385,300 (Miliyan daya da dubu dari uku da tamanin da biyar, da naira dari uku).
To da zarar ka mallaki kudin da suka kai haka, kuma suka shekara ahannunka, to shikenan zakkah ta wajabta akanka. Zaka raba kudin naka zuwa kashi arba'in sannan ka fidda kashi guda ka raba atsakanin Talakawa sa Miskinai da sauran wadanda Allah ya lissafa dasu.

No comments

Powered by Blogger.